MDD Ta kira Yi Mutanen Zimbabwe Da Su Kai Zuciyar Nesa
Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana damuwarsa akan rikicin da ya kunno kai bayan zaben shugaban kasa a Zimbabwe yana kiran al'ummar kasar da su kai zuciya nesa.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya nakalto babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniyar yana yin kira ga 'yan siyasa da al'ummar kasar da su kauce wa tashin hankali,kuma su yi amfani da hanyoyin zaman lafiya domin warware sabanin da ake da shi akan sakamakon zaben.
Tashin hankali ya barke a kasar ta Zimbabwe bayan sanar da cewa jam'iyya mai mulki a kasar ta Zanu PF ce ta sami rinjaye a zaben 'yan majalisa da na shugaban kasa.
Sakamakon zaben ya bayyana shugaban kasa mai ci Emmerson Mnangagwa a matsayin wanda ya zo na daya, sai kuma jagoran babbar jam'iyyar hamayya Nelson Chamisa a matsayin na biyu.