Sarkin Dubai Ya Soki Lamirin Mahukuntan Kasashen Larabawa
(last modified Mon, 06 Aug 2018 05:50:42 GMT )
Aug 06, 2018 05:50 UTC
  • Sarkin Dubai Ya Soki Lamirin Mahukuntan Kasashen Larabawa

Sheikh Muhammad Bin Rashid Al Maktum sarkin Dubai ya caccaki mahukuntan kasashen larabawa kan abin da ya kira rashin iya tafiyar da mulki a kasashensu.

Kamfanin dillancin labara Sputnik ya bada rahoton cewa, Sheikh Muhammad Bin Rashid Al Maktum sarkin Dubai, kuma Firayi ministan kasar hadaddiyar daular larabawa, ya soki mahukuntan kasashen larabawa tare da bayyana su a matsayin masu bata lokaci kawai.

Ya bayyana hakan ne a shafinsa na twitter, inda ya ce babban abin takaici ne yadda larabawa suka zama ba su iya tabuka ma kansu komai, sai dai su jira  a yi musu, alhali suna da dukkanin abin da suke bukata domin aiwatar da komai a kasashensu.

Sarkin na Dubai ya yi ishara da yadda suka dogara da kasashen yammacin turai a cikin dukkanin lamurransu, inda ya ce wannan mummunar siyasa ce shugabannin kasashen larabawa suka daukar wa kansu, wadda ba za fishe su ba.