Shugaban Kasar Syria Ya Yi Watsi Da Shawarar Kasar Saudiyya
(last modified Wed, 22 Aug 2018 19:01:31 GMT )
Aug 22, 2018 19:01 UTC
  • Shugaban Kasar Syria Ya Yi Watsi Da Shawarar Kasar Saudiyya

Wani dan majalisar dokokin Lebanon mai wakiltar Hizbullah ya ce; Shugaba Basshar Assad ya ki yarda da shawarar Saudiyya na yanke alaka da Hizbullah domin Saudiyya ta kashe makudan kudi saboda sake gina Syria

Nawwaf Musawi ya fada a yau Laraba cewa; Saudiyyar ta kawo sharadinta ne na zuba makudan kudi domin sake gina kasar Syria da yaki ya daidaita, amma shugaba Basshar Assad ya yi watsi da ita.

Dan majalisar na Hizbullah ya ce Basshar Assad dan gwagwarmaya ne don haka ya zabi ci gaba da kasantuwa tare da gwagwarmaya

Watanni uku da su ka gabata ne yarima mai jiran gado na Saudiyya Muhammad Bin Salman ya aike da dan sako zuwa ga shugaban na kasar Syria, kamar yadda rahoton ya nuna.

Sharadin na Saudiyya ya kuma kunshi lamintar kasar da Basshar Assad ya ci gaba da mulki har tsawon ransa matukar zai yanke alaka da Hizbullah da kuma kasar Iran.