An Zargi Amurka Da Shirin Kai Wa Syria Hari
Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ce ta sanar da cewa Amurkan tana girke kayan yaki kusa da Syria da shirin kai mata hari
Kamfanin dillancin labaran Sputnik ya nakalto Igor Konashenkov, mai magana da yawun ma'aikatar tsaron kasar ta Rasha yana cewa; An ga yadda Amurka take kara jan damarar yaki a kusa da iyakar kasar Syria wanda ga dukkanin alamu tana son kai wa Syrian hari ne.
Kakakin ma'aikatar tsaron kasar ta Syria ya kara da cewa; Abin da hakan yake nunawa shi ne 'yan ta'adda a kasar Syria suna son yin wani wasan kwaikwayo na kai hari da makamai masu guba domin su bai wa Amurkan damar kai hari.
A cikin watan Aprilu na 2018 'yan ta'addar sun shirya wani wasan kwaikwayo na kai hari da makamai masu guba wanda ya sa kasashen Amurka, Birtaniya, Faransa su ka kai wa Syria hari.