An Bukaci Yanke Wa Fitaccen Malamin Salafiyya Na Saudiyya Hukuncin Kisa
Babban mai shigar da kara na Saudiyya ya bukaci da kotun ta yanke hukuncin kisa akan Sheikh Salman Audah a yau Talata.
Jaridar Ukkaza da ake bugawa a Saudiyyar ta ba da labarin cewa an fara yi wa Sheikh Salman Audha sharia ne a kotun manyan laifuka ta kasar.
Shekara daya da ta wuce kenan da kame malamin wanda yake da fiye da mutane miliyan biyar masu bibiyarsa a shafinsa na Twitter.
Gwamnatin Saudiyya tana daukar Audha wanda shi ne mataimakin shugaban kungiyar malaman musulmi ta duniya, a matsayin dan ta'adda.
Baya ga Salmanul Audha da aka kama a 2017, da kawai wasu mutane 10 da su ka hada malaman addini da kuma masu rajin kare hakkin dan'adam.
Kasashen duniya ne suna yin kiraye-kiraye akan kasar Saudiyya da ta saki mutanen da ta kama ko kuma a yi musu shari'a mai adalci.