Italiya Tana Binciken Yadda Gwamnatocin Baya Suka Sayarwa Saudia Makamai
(last modified Sat, 29 Sep 2018 19:03:04 GMT )
Sep 29, 2018 19:03 UTC
  • Italiya Tana Binciken Yadda Gwamnatocin Baya Suka Sayarwa Saudia Makamai

Ministan harkokin tsaron kasar Italiya ta bayyana cewa za'a gudanar da bincike don gani yadda gwamnatocin kasar a baya suka sayarwa kasar saudia makamai.

Majiyar muryar JMI ta nakalto Elisabetta Trenta ministan tsaron kasar Italiya tana fadar haka, a yau Asabar ta kuma kara da cewa idan kasar saudia ta sabawa sharuddan da aka cimma da ita wajen sayar mata boma boman da kamfanonin kasar suke kerawa tana iya dakatar da sayarwa kasar karan makamai.

Kasashen Britania, Jamus da Italiya na daga cikin kasashen turai da suka fi sayarwa kasar Saudia makamai wadanda take kashe mutanen Yemen da su a halin yanzu.

Matsayin da ministan tsarin kasar Italiya ta dauka ya sami amincewar wasu daga cikin yan majalisar dokokin kasar Italiya.

Tun cikin watan Maris na shekara ta 2015 ne kasar saudia da kawayenta na kasashen larabawa suka farwa kasar Yemen da yaki wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla dubu 14 sannan ya jefa miliyoyin mutanen kasar cikin tsananin yunwa.