An Kashe Sojojin Saudiyya Da Dama A Yemen
-
wani wuri da aka kai hari
An Kashe Jami'an Sojan Kasashen Saudiyya A Kasar Yemen
Sojojin Kasashen Waje da su ke yaki a cikin kasar Yemen da dama sun halaka a yau juma'am.
Tashar Telbijin din almayadeen mai watsa shirye-shiryenta daga kasar Lebanon, ta ambato majiyar sojan kasar Yamen na cewa; A tsakanin wadanda su ka halaka sanadiyyar harin da makami mai linzami da su ka kai a sansanin Mas' da ke gundumar Ma'arib, a yau juma'a da akwai manyan jami'an sojan Saudiyya 2 da kuma na Hadaddiyar Daular Larabawa 3.
Tun da fari tashar telbijin din almasirah, ta kungiyar Ansarullah a Yemen ta ambaci cewa; Adadin wadanda su ka mutu a harin da su ka kai wa sansanin na Mas, sun kai 105, tsakanin sojojin Saudiyya da na Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma sauran sojojin haya.
Kusan shekara guda kenan dai da saudiyya da kawayenta su ka shelanta yaki akan al'ummar kasar Yemen, wanda kawo ya zuwa yanzu su ka kashe dubbai daga cikinsu mafi yawancinsu fararen hula da kananan yara.