Dan Kunar Bakin Wake Ya Kashe Dan Takara A Afganistan
(last modified Wed, 10 Oct 2018 05:42:18 GMT )
Oct 10, 2018 05:42 UTC
  • Dan Kunar Bakin Wake Ya Kashe Dan Takara A Afganistan

Rahotanni daga Afganistan na cewa wani harin kunar bakin wake ya yi ajalin mutum 8, da kuma raunana wasu 11, a wani ofishin dan takara zaben 'yan majalisar dokoki a garin Lashkar Gah dake yankin Helmand a kudancin kasar.

Daga cikin wadanda harin ya yi ajalinsu har da wani dan takara zaben 'yan majalisar dokokin kasar mai suna Saleh Mohammad Asikzai, kamar yadda kakakin gwamnan yankin Omar Zhwak ya tabbatarwa kamfanin dilancin labaren AFP.

Babu dai wata kungiya data dau alhakin kai harin kawo yanzu, saidai hakan na zuwa ne kwana guda bayan da kungiyar 'yan ta'adda ta Taliban ta fitar da sanarwar shan alwashin cutura da zaben 'yan majalisar dokokin kasar dake tafe.

Hakan dai ya sanya adadin 'yan takaran da aka kashe a cikin irin wannan yanayin ya kai zuwa shida a cewar hukumar zaben kasar.

Sama da 'yan takara 2 500 zasu fafata a zaben 'yan majalisar dokokin kasar ta Afganistan da za'a gudanar a ranar 20 ga watan Oktoban nan.