Palastiwa 7 Sun Yi Shahada A Yankin Zirin Gaza
(last modified Fri, 12 Oct 2018 19:15:28 GMT )
Oct 12, 2018 19:15 UTC
  • Palastiwa 7 Sun Yi Shahada A Yankin Zirin Gaza

Jami'an tsaron haramtacciyar kasar Isra'ila sun buda wuta kan Palastinawa a arewa da gabashin yankin zirin Gaza, lamarin da ya yi sanadiyar shahadar 7 daga cikin su da kuma jikkata wasu dama na daban.

Kafar watsa labaran Palastinu ta habarta cewa a daren jiya alhamis, wasu matasan Palastinawa sun taru a yakin kan iyalan zirin Gaza domin tattaunawa yadda za su gudanar da zanga-zangar neman dawo da hakki,saidai jami'an tsaron HK Isra'ila sun kai musu farmaki inda suka bindige 4 daga cikinsu har lahira tare kuma da jikkata wani adadi daga cikinsu.

A yayin zanga-zangar ta neman dawo da hakki da ya gudanar yau juma'a a kan iyaka da zirin Gazan wasu uku daga cikin Palastinawa sun yi shahada  bayan da jami'an tsaron Sahayunan suka buke musu wuta.

Daga  watan Maris zuwa yanzu sama da Palastinawa 200 ne suka yi shahada  yayin da wasu sama da dubu 21 na daban suka jikkata ta hanyar harsashen Sojojin Sahayuna, a yayin zanga-zangar lumana da Palastinawa suka yi na nemo da hakkiin kasarsu.

Da dama daga cikin kasashen Duniya ciki harda jamhoriyar musulinci ta Iran da kuma kungiyoyin kasa da kasa sun yi tofin alatsinai da ta'addancin Sahayunan.

Palastinawa na gudanar da zanga-zangar ne a yayin zagayowar ranar da Sahoyuna suka dauki kudirin kwace kasar palastinu a ranar 30 ga watan Maris shekarar 1976, a shekarar bana dai al'ummar yankin zirin Gaza sun kudiri gudanar da zanga-zangar a ko wata ranar juma' a har lokacin da su samu nasarar kan sahayunan, inda a yau  juma'a ma suka gudanar da zanga-zangar .