Saudiyya: An Kame Yarimomi 5 Saboda Kin Yarda Da Kisan Kashoogi
(last modified Sat, 13 Oct 2018 19:04:27 GMT )
Oct 13, 2018 19:04 UTC
  • Saudiyya: An Kame Yarimomi 5 Saboda Kin Yarda Da Kisan Kashoogi

Rahotanni daga Saudiyya sun ambaci cewa; An kame yarimomin biyar zuwa wani wuri da ba san ko'ina ba ne, saboda sun nuna kin amincewa da kisan dan jaridar kasar Jamal Kashoogi a kasar Turkiya

Yarima Khalid Bin Farhan ali-Saud wanda yake zaune a kasar Jamus, ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa;  Gwamnatin Saudiyya tana gayyatar wadanda take adawa da su domin tattaunawa, amma a karshe ta yi awon gaba da su.

Khalid Bin Farhan ali Sa'ud ya kuma bayyana cewa; Kwanaki goma gabanin bacewar Jamal Kashoogi, an tsara sace shi, inda su ka gayyace shi da ya je ofishin jakadancin kasar da ke Masar domin a ba shi miliyoyin daloli.

Bayan da Muhammad Bin Salman ya zama yarima mai jiran gado, yarima Khalid Bin Farhan ya fice daga cikin kasar Saudiyya inda ya nemi mafaka a kasar Jamus.

Yarima Khalid ya kira yi al'ummar Saudiyya da su yi wa gwamnatinsu tawaye matukar ta tabbata tana da hannu a kisan Jamal Kashoogi.