Saudiyya: An Kame Yarimomi 5 Saboda Kin Yarda Da Kisan Kashoogi
Rahotanni daga Saudiyya sun ambaci cewa; An kame yarimomin biyar zuwa wani wuri da ba san ko'ina ba ne, saboda sun nuna kin amincewa da kisan dan jaridar kasar Jamal Kashoogi a kasar Turkiya
Yarima Khalid Bin Farhan ali-Saud wanda yake zaune a kasar Jamus, ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa; Gwamnatin Saudiyya tana gayyatar wadanda take adawa da su domin tattaunawa, amma a karshe ta yi awon gaba da su.
Khalid Bin Farhan ali Sa'ud ya kuma bayyana cewa; Kwanaki goma gabanin bacewar Jamal Kashoogi, an tsara sace shi, inda su ka gayyace shi da ya je ofishin jakadancin kasar da ke Masar domin a ba shi miliyoyin daloli.
Bayan da Muhammad Bin Salman ya zama yarima mai jiran gado, yarima Khalid Bin Farhan ya fice daga cikin kasar Saudiyya inda ya nemi mafaka a kasar Jamus.
Yarima Khalid ya kira yi al'ummar Saudiyya da su yi wa gwamnatinsu tawaye matukar ta tabbata tana da hannu a kisan Jamal Kashoogi.