Tasirin Kisan Jamal Khashuggi Kan Masarautar Saudia
(last modified Sun, 21 Oct 2018 02:37:39 GMT )
Oct 21, 2018 02:37 UTC
  • Tasirin Kisan Jamal Khashuggi Kan Masarautar Saudia

A ranra 2 ga watan Octoban da muke ciki ne aka kashe Jamal Khashuggi wani dan jarida a karamin ofishin jakadancin Saudia da ke birnin Santanbul na kasar Turkiya. Sannan ya tabbata ga ko wa daga ciki har da shugaban kasar Amurka Donal Trump kan cewa Mohammad bin Salman yerima mai jiraran kadon kasar ta saudiya shi ne ya bada umurnin kisan. Sannan hatta gwamnatin kasar Amurka a wannan karon ta kasa kare shi daga aikata laifi.

Wannan ya sa mafi yawan kasashen duniya suka yi ca a kan kasar ta Saudia, Amma tasiri mafi girma shi ne yadda 'ya'yan gidan sarautar kasar suka fara rige-rigen neman kujerar Muhammad bin Salman idan har aka sauke shi.

Jaridar St. Galler Tagbalatt na kasar Jamus ta rubuta dangane da wannan batun kan cewa, " a cikin watan Octoban da muke ciki ne Muhammad Binn Salman ya shirya wani taro na kasa da kasa a birnin Riyad don samar da masu zuba jari a cikin tattalin arzikin kasar saudia, amma ga shi yanzu ba batun taron ya dame shi ba, don kujerarsa ce take girgiza ko zai tsira ko ba zai tsiri ba Allah ya sani. 

Wasu rahotanni sun bayyana cewa sarki salman yana son maye gurbin Mohammad da kaninsa Khalid wanda a halin yanzu yake rike da matsayin jakadan kasar Saudia a Amurka.

Har'ila yau wani marubuci a jaridar washingtonpost ta kasar Amurka ya bayyana cewa akwai wasu labarai da suke cewa 'yayan gidan sarautar ta saudia suna son a nada Ahmad bin Abdulaziz dan sarki Abdulaziz wanda ya kafa sarautar ta saudiya.

Duk da cewa ba za'a ce a yanke Muhammad bin Salman zai sauka daga kujerar yerima mai jiran gadon sarauta ba, amma kuma kisan Jamal Khashaggi ya yi sanadiyyar girgizan kujerarsa, kuma bayan fadawa kasar Yemen da yaki da yake jagoranta,  kisan Jamal Khashaggi yana daga cikin manya manyan kura kuran muhammad bin Salman ya aikata a cikin shekaru 2 da ya yi yana rike da wannan mukamin. 

Sai dai duk daga haka Sarki Salman da dansa Muhammad suna iya kokarinsu don dorawa wasu jami'an gwamnatin kasar don kubutar da Muhammad din daga matsalar da ya jefa kansa a ciki. Daga cikin wadanda abin zai shafa sun hada da Adil Aljubair ministan harkokin wajen kasar ta Saudia, ganin cewa ya kasa yin wani abu na kare Muhamman bin salman kan wannan zargin, yau kwanaki 17 da faruwarsa. Kuma tuni an bada sanarwan cewa sabani ya shigo tsakaninsa da shi Mohamad bin Salman. 

Danga ne da wannan labarin jaridar "Nuwai-Wakt" ta kasar Pakistan ta rubuta cewa a wani taron majalisar ministocin da sarkin Salman da kansa ya jagoranta, an zabi Nuwaaf Sa'eed Almaaliki jakadan kasar ta saudia a kasar Pakistan a matsayin sabon ministan harkokin wajen kasar wanda zai maye gurbin Adil aljubair. 

Har'ila yau akwai batun ajiye aiki na jakadan kasar ta Saudia a birnin Istambul wannan aka kashe Jamal a ofishinsa. daga karshe muna iya cewa sauka da sauye sauyen mukamai a masarautar ta saudia suna iya kubutar da Muhammad bin Salman daga halin da ya fada ciki na wani lokaci, amma kuma karfinsa ya ragu sosai idan an kwatanta da watannin 45 na baya da yake rike da wannan mukamin.