'Ya 'Yan Kashoggi Sun Bukaci A Mika Masu Gawar Mahaifinsu
(last modified Mon, 05 Nov 2018 11:13:58 GMT )
Nov 05, 2018 11:13 UTC
  • 'Ya 'Yan Kashoggi Sun Bukaci A Mika Masu Gawar Mahaifinsu

'Ya 'yan dan jaridan nan na Saudiyya da aka kashe, sun bukaci hukumomin Saudiyya dasu mika masu gawar mahaifinsu, ta yadda iyalansa zasu yi masa zaman makoki, kamar yadda suka sanar a gdian talabijin na CNN.

Wani dan uwan dan jaridan mai suna Salah ya ce suna son binne mirigayin a makabartar Al Baki dake Madina.

A ranar 2 ga watan Oktoba da ya gabata ne aka kashe dan jaridan a cikin karamin ofishin jakadancin Saudiyyar a birnin Santambul na Turkiyya. 

Mahukuntan Turkiyya dai sun danganta kisan da shiryayen abu, da ya samu umarni daga kololuwar gwamnatin Saudiyya.