'Yan Siriya 20,000 Sun Makale Akan Iyaka Da Turkiyya
-
dakaru na tare \'yan gudun hijira
Kusan mutane 20,000 da su ka kwararo daga cikin kasar Syria, sun makale akan iyaka da kasar Turkiya
Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa a halin da ake ciki a yanzu da akwai mutane kusan 20,000 da su ka kwararo daga cikin kasar syria, sun makale akan iyakar da kasar Turkiya.
Mai magana da yawun hukumar bada agaji ta majalisar dinkin duniya, Linda Tom ta ce; Hasashen farko ya tababtar da cewa; da akwai mutane dubu 20,000 da su ka taru a kan iyakar ta Turkiya, sai kuma wasu da adadinsu ya kai 15,000 da suka kwararo daga garin A'azaz a gundumar Halab, da sojojin Syria ke kai wa farmaki a arewacin kasar.
Bugu da kari, mai magana da yawun hukumar bada agajin ta majalisar dinkin duniyar ta kuma yi kirdadon cewa za a iya samun wasu mutanen da adadinsu zai kai 10,000 wadanda za su shiga garin Irfin da ke karashin ikon Kurdawa.
Hukumar Bada Agajin ta sha alwashin fadada cibiyoyinta na bada agaji ayankin domin taimakawa 'yan gudun hijirar.
Tun daga ranar litinin ne dai sojojin na Syria da kawayensu su ka tsananta kai farmaki a gundumar Halab, da hakan ya basu damar kwace garuruwa da dama.