Kungiyar "Afuwa" Mai Rajin Kare Hakkin Dan'adam Ta Soki Kasar Saudiyya
Kungiyar ta yi suka akan yadda ake kame masu kare hakkin bil'adama da kuma azabtar da su a cikin kasar ta Saudiyya
Ita ma kungiyar kare hakkin bil'adama ta "Human Right Watch" ta soki jami'an tsaron kasar Saudiyya da yi wa wasu mata masu rajin kare hakkin dan'adam fyade tare da kuma azabtar da su.
Rahoton kungiyar Amnesty ya ambato wasu shaidu da suka tabbatar da cewa ana azabtar da wasu mutanen ta hanyar jona musu wutar lantarki.
Dukkanin kungiyoyin biu dai sun zargi jami'an na Saudiyya da yi wa mata masu rajin kare hakkin dan'adam fyade.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da kungiyoyin kare hakkin bil'adama suke fitar da rahoto dangane da yadda ake cin zarafin bil'adama a cikin kasar Saudiyya.
A halin da ake ciki a yanzu, da akwai fursunonin siyasa da su ka dai dubu talatin da ake tsare da su a gidajen kurkuku kasar daban-daban.