Taliban Ta Hallaka Sojin Amurka 3 A Afganistan
Kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai harin bam din da ya hallaka wasu sojin Amurka uku a birnin Ghazni dake tsakiyar kasar Afganistan.
Wata sanarwa da kungiyar ta fitar a manhajar WhatsApp, ta bakin kakakinta, Zabihullah Mujahid, ta ce ita keda alhakin kai harin kan ayarin sojojin na Amurka.
Duk da cewa dai tawagar sojin Amurka a kungiyar tsaro na NATO bata yi karin haske ba kan lamarin, amma rahotanni sun nuna cewa wani bam ne kirar gargajiya da aka dana ya tashi da sojojin na Amurka inda uku daga cikinsu suka hallaka, kana wasu uku na daban suka raunana.
Wannan dai ya sanya adadin sojin Amurka da aka kashe a kasar ta Afgasnitan tun daga farkon wannan shekara ya kai guda 12.
Amurka dai ta rasa sojoji sama da 2 400 tun bayan data sanya kafa a Afgasnitan a cikin shekara 2001, domin kawokarshen mulkin 'yan Taliban a lokacin.