Human Rights Watch, Ta Bukaci A Kame Muhammad Ben Salman
(last modified Wed, 28 Nov 2018 05:02:42 GMT )
Nov 28, 2018 05:02 UTC
  • Human Rights Watch, Ta Bukaci A Kame Muhammad Ben Salman

Kungiyar kare hakkin dan Adama ta kasa da kasa (Human Rights Watch), ta shigar da wata kara gaban kotun Argentina kan yarima mai jiran gado na Saudiyya, Muhammad ben Salmane, da ake zargi da hannu a kisan dan jaridan nan Jamel Khashoggi da kuma aikata laifukan yaki a kasar Yemen.

Kungiyar ta (HRW), ta bukaci Argentina data yi amfani da damar da kundin tsarin mulkinta ya bayar kan laifukan cin zarafin bil adama, domin kama yarima Ben Salmane din wanda zai ziyarci kasar a ranar Juma'a mai zuwa domin halartar taron G20. 

Bayanai dai sun nuna cewa tuni hukumomin shari'a na Argentina suka soma nazari kan karar da kungiyar ta (Human Rights Watch), ta shigar kan alakar yarima Muhammad ben Salmane kan laifukan yaki da kawancen da kasarsa ke jagoranta kan Yemen da kuma batun azabtarwa na jami'an Saudiyya ga dan jaridan kasar Jamel Khashoggi.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da Mohammed ben Salman ya fara ziyara a wasu kasashen Larabawa ciki harda na yankin Magreb, da suka da Tunisia da Aljeriya, wacce ita ce ta farko tun bayan lamarin kisan dan jaridan a karamin ofishin jakadancin Saudiyya na Santambul dake Turkiyya a farkon watan Oktoba da ya gabata.

A jiya ma dai dubban al'ummar kasar Tunusiya ne suka gudanar da wata gagarumar zanga-zangar kin jinin ziyarar ta Yarima mai jiran gado na Saudiyya, saboda wadannan zarge zarge da ake masa.

Kasar Saudiyya dai na ci gaba da musanta hannun yarimanta a kisan dan jaridan.