Khashoggi / Yemen : Saudiyya Ta Yi Tir Da Kudirin Majalisar Dattijan Amurka
Saudiyya tayi allawadai da da kudurorin da 'yan majalisar dattijan Amurka suka amince dasu kan kisan dan jaridan nan Jamel Khashoggi da kuma rikicin Yemen.
A wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta fitar, Saudiyya ta yi watsi da dukkan kudurorin majalisar wanda ta ce basu da tushe balle makama, hasali ma shishigi ne a harkokin cikin gidan kasar.
A ranar Alhamis data gabata ne 'yan majalisar dattijai na Amurka, suka amince da gagarimin rinjaye da wani kudiri dake zargin yarima mai jiran gado na Saudiyyar, Mohammad Ben Salman, da kisan dan jaridan nan mai sukar masarautar Saudiyyar, Jamal Khashoggi.
Kudirin ya kuma bukaci kawo karshen duk wani irin taimakon soji na Amurkar ga Saudiyya a yakin da take jagoranta a kasar Yemen.