Dan Uwan Sarkin Saudiyya, Yarima Talal ben Abdel Aziz, Ya Mutu
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i34528-dan_uwan_sarkin_saudiyya_yarima_talal_ben_abdel_aziz_ya_mutu
Hamshakin yariman nan na Saudiyya, Al-Walid ben Talal, ya sanar da rasuwar mahaifinsa, yarima Talal ben Abdel Aziz, wanda dan uwa ne ga Sarkin Saudiyya Salmane ben Abdel Aziz.
(last modified 2018-12-22T16:03:07+00:00 )
Dec 22, 2018 16:03 UTC
  • Dan Uwan Sarkin Saudiyya, Yarima Talal ben Abdel Aziz, Ya Mutu

Hamshakin yariman nan na Saudiyya, Al-Walid ben Talal, ya sanar da rasuwar mahaifinsa, yarima Talal ben Abdel Aziz, wanda dan uwa ne ga Sarkin Saudiyya Salmane ben Abdel Aziz.

Ben Talal, ya sanar da rasuwar mahaifinsa ne a shaffinsa na Twitter, inda yake cewa Allah ya yi wa mahaifinsa yarima Talal ben Abdel Aziz, rasuwa a yau Asabar, yana mai shekaru 87 a duniya.

An dai bayyana cewa a lokacin rayuwarsa yarima Talal, ya kasance mai gwagwarmaya ta neman sauyi a masarautar Saudiyya, ciki har da ganin mata sun zamu izinin tukin mota, wanda suka samu a wannan shekara.

Sannan kuma yarima Talal, ya rike shugabancin tsarin kasashen Larabawa na Golfe na kungiyoyin ci gaba na MDD (AGFUND) dake fafatukar wanzarda ilimi, kiwan lafiya da 'yancin mata a kasashe masu tasowa.

Baya ga hakan kuma ya kasance cikin harkar 'ya 'yan gidan sarauta masu 'yanci dake bukatar kawo sauyi a harkar asusun kudade a Saudiyya.