Kungiyoyin 'Yan Ta'adda A Kasar Syria Suna Fada Da Juna
A kalla mutane 500 su ka halaka a fadan da kungiyoyin ta'addanci suke yi a tsakaninsu a kasar Syria
Rahotannin da suke fitowa daga yankin Halab na kasar Syria sun ce; An yi bata kashi mai tsanani a tsakanin kungiyoyin Tahrirus-sham da kuma Jabhatut-Tahriri, inda su ka rufe muhimman hanyoyin da suke a yankin
Har ila yau fadan da kungiyoyin 'yan ta'adda suke yi ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula 20 a yankin.
Sabani ya kunno kai a tsakanin kungiyoyin ne tun ranar farko ta watan nan na January a kusa da garin Taladah da ke arewa maso yammacin kasar Syria bayan da aka kashe 'yan kungiyar Tahrirus-Sham mai alaka da Jbhanus Nusrah
A watan Oktoba na shekarar da ta gabata ma an yi wannan irin fadan a tsakanin kungiyoyin Nusrah da Nuruddin Zanki