Italiya Na Shirin Sake Bude Ofishin Jakadancinta A Kasar Syria
(last modified Sun, 13 Jan 2019 07:16:57 GMT )
Jan 13, 2019 07:16 UTC
  • Italiya Na Shirin Sake Bude Ofishin Jakadancinta A Kasar Syria

Gwamnatin kasar Italiya ta sanar da cewa, tana da shirin sake bude ofishin jakadancinta abirnin Damascus na kasar Syria.

Ministan harkokin wajen kasar ta Italiya  Enzo Moavero Milanesi ne ya sanar da hakan a jiya, inda ya bayyana cewa, an samu kyautatar lamurra  akasar Syria, saboda haka sake bude ofishin jakadancin Italiya  akasar ta Syria abu ne mai matukar muhimmanci ga gwamnatin Italiya.

Wannan furuci na ministan harkokin wajen kasar ta Italiya na zuwa ne a daidai lokacin da kasahen turai da dama suke ta hankoron ganin sun sake mayar da alakarsu da Syria, bayan da suka yanke alakar tun a cikin shekara ta 2011.

Wasu daga cikin kasashen larabawa da suka yanke alaka da Syria, sun sanar da mayar da alakar tasu tare da sake bude ofisoshin jakadancinsu a Damascus, daga ciki kuwa har da wadanda suka taka rawa wajen daukar nauyin 'yan ta'adda a kasar ta Syria.