Kungiyar Kasashen Labarabawa Zata Mai Kasar Siriya Cikin Kungiyar
(last modified Fri, 18 Jan 2019 06:43:55 GMT )
Jan 18, 2019 06:43 UTC
  • Kungiyar Kasashen Labarabawa Zata Mai Kasar Siriya Cikin Kungiyar

Kungiyar kasara Larabawa ta bada sanarwan cewa zata sake dawo da kasar Siriya cikin kungiyar nan ba da dadewa ba.

kamfanin dillancin labarann IRNA na kasar Iran ya nakalto babban sakatarin kungiyar Ahmad Abu-Gaid yana fadar haka a safiyar yau Jumma'a a birnin Beyrut na kasar Lebanon inda yake halattar taron tattalin arziki na kasashen larabawa. 

Abu gaid ya kara da cewa da zaran dukkan kasashen kungiyar sun maince da sake dawo da kasar Siriya cikin kungiyar dai zai sanar da gwamnatin kasar Siriya hakan. 

A shekara ta 2011 ne kungiyar ta kore gwamnatin kasar Syriya karkashin shugabancin Bashhar Al-Asad wanda yake fafatawa da yan ta'adda wadanda wasu kasashen larabawan da kawayensu suke goyon bayan yan ta'addan.

Kasashen Saudia da hadaddiyar daular Larabawa ne suka matsawa kungiyar ta kori kasar Siriya daga kungiyar sannan ta bawa kujerar kasar ga yan tawaye wadanda suke yakar gwamnatin Bashsar Al-Asad. 

Amma yanzun da shugaban tare da kawayen kasashen Siriya suka sami nasara a kan yan ta'addan , ko wace kasa daga cikin kasashen na larabawa suna rige-rigen sake bude ofisoshin jakadancinsu a birnin Damesh