Jan 21, 2019 19:19 UTC
  • An Jikkata Sojojin Amurka Biyu A Arewa Maso Gabashin Siriya

Rahotani dake fitowa daga kasar Siriya sun sanar da tarwatsewar wata mota shake da bama-bamai a kan hanyar dakarun kasar Amurka a lardin haskah na arewa maso gabashin kasar, lamarin da ya yi sanadiyan raunana sojojin Amurka biyu.

Tashar talabijin din Rasha ta habarta cewa a wannan Litinin wata mota shake da bama-bamai ta tarwatse a lardin Haskah na kasar Siriya kusa da  tawagar dakarun tsaron Amurka lamarin da ya yi sanadiyar jikkatar sojojin Amurka biyu.

Har ila yau Kamfanin dillancin labaran Hawar na kurdawan kasar Siriya ya habarta cewa dakarun tsaron na Kurdawa sun yi kokarin tsayar da motar bayan da suka yi shakku kanta, amma tayi tsayawa har saida ta isa wani shingen bincike na jami'an tsaron hadin gwiwar  sojojin Amurka da kurdawa.

A bangare guda, kungiyar rajin kare hakin bil-adama ta kasar Siriya ta sanar da cewa ya zuwa yanzu harin kunar bakin waken ya yi sanadiyar hallaka dakarun kurdawa biyar da kuma jikkata sojojin Amurka biyu.

Wannan dai shi ne karo na biyu cikin mako guda kacal,  da ake kaiwa Sojojin Amurkan hari a yankunan kurdawa na kasar Siriya, inda a ranar larabar da ta gabata, wata mota shake da bama-bamai ta tarwatse a kusa da motocin sintiri na dakarun tsaron Amurka a garin Manbij dake arewacin kasar Siriya, lamarin da ya yi sanadiyar hallakar sojojin Amurka biyar da na majalisar tsaron garin Manbij 18.

Tuni dai kungiyar ta'addancin nan ta ISIS ta dauki alhakin kai harin.

 

 

 

Tags