Jul 16, 2018 18:13 UTC
  • Jiragen Yakin Kawancen Amurka Na Ci Gaba Da Kai Hari A Siriya

Jiragen yakin kawancen Amurka sun yi ruwan bama-bamai kan kauyen Assusa na jihar Dairu-Zur tare da kashe fararen hula a wannan Litinin.

Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya habarta cewa a wannan Litinin jiragen yakin kasa da kasa karkashin jagorancin Amurka dake da'awar yaki da kungiyar ISIS a Siriya sun ci gaba da kai hari kan gidajen farar hula a kauyen Assusa na jihar Dairu-Zur , inda suka kashe mutum biyu na gida guda da kuma jikkata wasu dama na daban cikin harda mata da kananen yara.

A kwanaki ukun da suka gabata ma, jiragen yakin kawancen Amurkan sun kai irin wannan mumunan hari a garin Boukmal na jihar Dairu-Zur dake kai iyakar Sirya  da kasar Iraki, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutune sama da 50 tare da jikkata wasu da dama na daban daga cikinsu akwai Mata da kananen yara.

A watan Augustan 2014 ne jiragen yakin kasa da kasa karkashin jagorancin Amurka bisa da'awar yaki da kungiyar ISIS suka tare a kasar Siriya inda ya zuwa yanzu suka kashe fararen hula da dama da basu ji ba su gani ba a jihohin Rakka, Dairu-Zur da Halab.

Tags