Turkiyya : An Cafke Masu Alaka Da Gülen, Sama da 600
(last modified Tue, 12 Feb 2019 15:25:49 GMT )
Feb 12, 2019 15:25 UTC
  • Turkiyya : An Cafke Masu Alaka Da Gülen, Sama da 600

Rahotanni daga Turkiyya na cewa, akalla mutum 641 ne da aka cafke bisa zarginsu da alaka da shehun malamin nan na kasar, Fethullah Gülen, wanda gwamnatin Ankara ke zargi da hannu a yunkurin juyin mulkin watan Yuli na 2016 da bai yi nasara ba.

Hakan dai a cewar kamfanin dilancin labaren Anadolu, ya biyo bayan da ofishin mai gabatar da kara na gwamnatin ta Ankara ya aike da sunayen mutane 1,112 da ake wa wannan zargin ga mahukuntan na kananen hukumomi 75 da kuma larduna 81 na kasar ta Turkiyya.

Kuma a cewar labarin hakan na daga cikin binciken da ake kan fitar da wata zanawar jarabawa ta shiga aikin 'yan sanda a shekara 2010, wacce ake zargin magoyan bayan malamin Fethullah Gülen.

Dama dai kafin hakan, ministan cikin gida na kasar ta Turkiyya, Süleyman Soylu, ya bayyana a ranar Lahadi data gabata cewa, za'a kaddamar da wani sabon samame kan magoyan bayan shehun malamin, da nufin kakkabesu gabadaya daga kawar.

Hukumomin Turkiyya na zargin shehun malamin Gülen, da kisa juyin mulkin da bai yi nasara ba a ranar 15 ga watan Yuli na shekara 2016, zarginda shehun malamin da ya kwashe kusan shekaru ashirin yana zama a Amurka, na ci gaba da musanta hannunsa a yunkurin juyin mulkin.