Mar 05, 2019 04:45 UTC
  • Rashin Zaman Lafiya Ne Ke Karfafa Ta'addanci A Kasashen Larabawa

Kungiyar kasashen Larabawa ta bayyana rashin zaman lafiya a wasu kasashe mambobinta, ne ke kara karfafa ayyukan ta'addanci musamman na kungiyar Da'esh a yankin.

Babban sakataren kungiyar ne, Ahmed Aboul Gheit, ya bayyana hakan, a yayin taron ministocin shari'a dana cikin gida na kungiyar da ya gudana ranar Litini a birnin Tunis.

Taron na Tunus wanda shi ne irinsa na uku, ya maida hankali ne kan hadda kasashen larabawan zasuyi hadin guiwa tsakaninsu wajen yaki da muggan laifuka.

Sanarwar karshen taron kasahen larabawan ta ce ta'addanci shi ne babban kalubalen dake a gabansu, duk da cewa ta yaba da yadda aka karya laggon kungiyar a baya bayan nan.

A yayin taron, kasashen sun cimma yarjejeniyi guda biyu da suka shafi yaki da safara mutane, da yaki da kuma kafa wata kungiya ta yaki da safara sassan jikin mutane.

Saidai ministocin cikin gida na kasashen da suka hada da Aljeriya, Masar, Qatar, Kowait da kuma Yemen basu halarci taron ba.

Tags