Mar 07, 2019 15:27 UTC
  • Kwamitin Zabe A H.K Isra'ila Ya Yi Watsi da Takarar Kawancen Larabawa

Kwamitin shirya zabe a haramtacciyar kasar Israila, ya yi watsi da takarar kawancen jam'iyyun larabawa a zaben 'yan majalisar dokoki na ranar 9 ga watan Afrilu mai zuwa.

Kwamitin zaben na zargin kawancen na Raam-Balad da goyan bayan ayyukan ta'addanci.

Saidai kuma a daya bangaren ya amince da takarar Michael Ben-Ari, jagoran jami'iyyar ''Jewish force party'', ta yahudawa wacce aka jima ana zargi da nuna kabilanci da kyammar larabawa.

kafin hakan dai firaministan Isra'ilar, Benjamin Netanyahu, ya bayyana a shafinsa na tweeter cewa duk jam'iyyar da bata kaunar yahudawa, ba tada gurbi a majalisar dokokin yahudawan ta Knesset.

Su dai Larabawan Isra'ila sun samo asali ne daga al'ummar Palasdinu da suka tsaya a Isra'ila bayan kafa ta a shekara 1948, kuma a halin yanzu suna a matsayin kaso 17,5% na al'ummar Isra'ila.

Tags