Mar 10, 2019 15:44 UTC
  • Musulmi Fiye Da Dubu 40 Suka Yi Sallar Juma'a A Masallacin Quds

Fiye da masallata dubu 40 ne suka yi sallar Juma’a a masallacin aqsa mai alfarma a wannan mako.

Kamfanin dillancin labaran Palastine ya bayar da rahoton cewa, duk da irin tsauraran matakan da jami’an tsaron yaudawa suka dauka, amma fiye da masallata dubu 40 ne suka yi sallar Juma’a a wannan mako a masallacin aqsa mai alfarma da kewaye.

Tun kafin wannan lokacin dai jami’amn tsaron yahudawan sun kafa shingayen tsaro da kuma bincike, domin hana falastinawa isa cikin masallacin.

Daga cikin irin matakan da suke dauka har da hana matasa da kuma wadanda shekarunsu ba su haura arba’in ba shiga cikin harabar masallacin, amma duk da hakan dubban musulmi sun samu damar shiga cikin masallacin da harabarsa kuma sun yi sallar Juma’a.