Mar 13, 2019 05:43 UTC
  • MDD Ta Fitar Da Rahoto Kan Kisan Fararen Hula 22 Da Saudiyya Ta Yi A Yemen

Babbar jami'ar majalisar dinkin duniya mai kula da ayyukan jin kai a kasar Yemen ta fitar da rahoto dangane da kisan fararen hula 22 da Saudiyya ta yi a ranar Lahadin da ta gabata, kamar yadda Shafin yada labarai na Al-khalij ya rawaito.

Data take sanar da hakan, babbar jami'ar majalisar dinkin duniya kan ayyukan jin kai a kasar Yemen Liz Grande ta ce, ta bi kadun abin da ya faru dangane da harin da jiragen yakin Saudiyya suka kaddamar a kauyen Kushar da ke cikin gundumar Hajjaha  a arewacin kasar Yemen.

Rahoton ya ce jami'an majalisar dinkin duniya sun ziyarci asibitocin da aka kai gawawwakin wadanda suka rasu da kuma wadanda suka samu raunuka, inda suka tabbatar da cewa kananan yara 12 da kuma mata 10 ne suka rasu sakamakon harin, yayin da wasu fiye da talatin suka jikkata.

Rahoton na tawagar majalisar dinkin duniya ya kara da cewa, jiragen na Saudiyya sun kai hare-haren ne a kan gidajen fararen hula, wadanda basu da wata alaka da ayyukan soji, kuma dukkanin wadanda suka rasu fararen hula da ba su san hawa ba su san sauka ba.