Mar 14, 2019 16:57 UTC
  • Saudiyya Ba Ta Amince Da A Yi Bincike Na Kasa Da Kasa Kan kisa Khashoggi Ba

Saudiyya ta bayyana rashin amincewarta da duk wani batun gudanar da bincike na kasa da kasa kan kisan Jamal Khashoggi ba.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, Bandar Bin Muhammad shugaban kwamitin da ake kira na kare hakkin bil adama a Saudiyya wanda masarautar kasar ta kafa, ya bayyana cewa kasar ba za ta taba amincewa da yunkurin da wasu suke na ganin sun mayar da batun kisan Khashoggi batu na kasa da kasa ba.

Wannan furuci ya zo ne  bayan kalaman da shugaban kasar Turkiya Rajab Tayyib Erdogan ya yi a jiya Laraba, inda ya ce sakamakon yadda masarautar Saudiyya take wasa da hankulan al'ummomin duniya kan kisan Khashoggi, ya zama wajibi a mayar da batun bincike kan wannan batu ya zama na kasa da kasa.

Bayan kisan Khasoggi a cikin ofishin jakadancin Saudiyya a Istanbul Turkiya a ranar 2 ga watan Oktoban 2018, gwamnatin Saudiyya ta musunta faruwar lamarin, amma bayan kusan makonni uku ta amince da kisan nasa, amma ta dora alhakin hakan akan wasu jami'an tsaro, tare da nisanta daga lamarin.