Mar 17, 2019 09:36 UTC
  • Kimanin Makamai Masu Linzami Dubu 500 Ne Aka Yi Amfani Da Su A Yemen

Cikin wani rahoto da ya fitar kakakin Rundunar tsaron kasar Yemen ya ce cikin shekaru 4 da suka gabata, Dakarun kawancen Saudiya sun kai hari sama da dubu 250 ta sama a kan fararen hula na kasar, sannan kuma sun halba sama da makamai masu Linzami da bama-bamai dubu 500 a kasar

Kamfanin dillancin labaran Irna ya nakalto Yahya Sari'i kakakin Rundunan tsaron Saudiya harwa yau yana cewa kawancen Saudiyan sun ruwan bama-baman da aka hana amfani da su sama da dubu 6 kan al'ummar kasar ta Yemen.

Har yanu dai dakarun kawancen Saudiya na amfani da makaman da aka hana amfani da su a Duniya kirar kasar Amurka da Birtaniya a kan al'ummar kasar Yemen din, amma Duniya ta yi shuru ba tare da daukan wani mataki ba.

Tun a watan Maris din 2015 ne kasar Saudiya tare da hadaddiyar daular larabawa bisa goyon bayan Amurka suka kaddamar da yakin wuce gona da iri kan al'ummar kasar Yemen, tare da killace kasar ta sama, kasa da kuma ruwa, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar Yamaniyawa akalla dubu 16 tare da jikkata wasu du ban na daban da kuma raba wasu milyoyi damahalinsu.