Mar 17, 2019 09:40 UTC
  • Tashin Nakiya Ya Yi Sanadiyar Mutuwa Da Jikkatar Mutum 40 A Siriya

Tashin Nakiyar da 'yan Ta'adda Suka binne a yayin da garin Deru-Zur na kasar Siriya ke karkashinsu ya yi sanadiyar mutuwar mutum 4 da jikkatar wasu 36 na daban.

Kamfanin dillancin labaran Irna ya habarta cewa a jiya assabar ne nakiyar ta tashin a yankin Shula na gefen kudu maso yammacin Deru-Zur dake gabashin kasar Siriya.

A yayin da 'yan ta'adda suka mamaye lardin Deru-Zur da sauran yankunan kasar Siriya, suka dana  bama-bamai da Nakiyoyi da ababen fashewa a gidajen fararen hula, hanyoyi da wuraren taruwar al'umma, motoci da babura, kai har ma da kayan wasanin kananen yara duk sun kasance tarkon bama-bama da abeben fashewa, lamarin dake nuna cewa sun mallaki irin wadannan abeben da dama.

Tun a shekarar 2011, kungiyoyin 'yan ta'adda dake samun goyon bayan Saudiya da kawayensu,suka tattauro 'yan ta'adda daga kasashen Duniya da nufin kawo karshen Gwamnatin Shugaba Asad, da hakan zai bawa Gwamnatin Sahayuna damar cin karanta ba babbaka.

Saidai a baya- bayan Sojojin kasar Siriya bisa taimakon masu bayar da shawara na dakarun tsaron jamhoriyar musulinci ta Iran da Rasha na samu nasarar kawo karshen kungiyoyin 'yan ta'adda a kasar.