Jan kunan Hizbullah ga kokarin raba kasar Siriya daga HKI
(last modified Mon, 18 Apr 2016 18:22:28 GMT )
Apr 18, 2016 18:22 UTC
  • Jan kunan Hizbullah ga kokarin raba kasar Siriya daga HKI

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lobnon ta ja kunan magabatan HKI a yunkurin da suke yi na raba kasar Siriya

A wata sanarwa da ta fitar yau kungiyar Hizbullah ta kasar Lobnon ta yi alawadai kan firicin Piraministan HKI Benjamin Natanyahu na mamayar da Haramcecciyar kasar sa ta yiiwa yankin Julan na kasar Siriya tare da jan kunansu kan yunkurin da suke yi na ganin an raba kasar ta Siriyan.

Sanarwar ta tabbatar da cewa wannan shike tabbatar da mumanar aniyar da Gwamnatin HKI ke da ita na mamaye kasashen Larabawa dake yankin, kuma wannan yunkurin nasu ba zai tabbata ba har abada.

Kungiyar Hizbullah ta tabbatar da cewa Magabatan HKI na daukan duk wasu matakan na ganin sun raba kasar ta siriya tare kuma da mamaye yankin Julan ya zame maso gurin tuntubar juna tsakaninsu da kungiyoyin 'yan ta'addar na Siriya.

Babban abin bakin ciki a nan shine yadda wasu daga cikin kasashen Larabawa ke iya kokarinsu wajen baiwa kungiyoyin 'yan ta'adda kudade da makamai domin ganin wannan manufa ta HKI ta tabbata.

A yayin zama da yayi tare ministocinsa Firaministan HKI Benjamin Natanyahu ya bayyana cewa sun mamaye yankin Julan kuma sun raba shi da kasar Siriya har abada ko da kasashen Duniya ba su amince ba.