Saudiyya : An Kori Ministan Ruwa Da Wutar Lantarki
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i4324-saudiyya_an_kori_ministan_ruwa_da_wutar_lantarki
Sarki Salmane na Saudiyya, ya kori ministan kula da sha'anin ruwa da wutar lantarki na kasar Abdallah Al-Hassine, inda tuni aka baiwa ministan gona na kasar umurnin jan ragamar wadanan fanonin.
(last modified 2018-08-22T06:58:10+00:00 )
Apr 24, 2016 23:59 UTC
  • sarkin Salmane bin Abdel-Aziz na Saudiyya
    sarkin Salmane bin Abdel-Aziz na Saudiyya

Sarki Salmane na Saudiyya, ya kori ministan kula da sha'anin ruwa da wutar lantarki na kasar Abdallah Al-Hassine, inda tuni aka baiwa ministan gona na kasar umurnin jan ragamar wadanan fanonin.

Wannan dai na zuwa bayan soma aiwatar da shirin gwamnatin kasar na rage tallafin wutar lantarki da ruwan sha da dai sauran su.

Masarautar Saudiyya dai ta dau wannan matakin ne wanda ba'a taba ganin irin sa ba saboda durkushewar tattalin arzikin ta sakamakon faduwar farashin man fetir din da ta dogara dashi.

koda yake labarin bai kawo dalilan sallamar ministan ba, aman wasu masu sharhi kan lamuran yau da kulun na ganin hakan baya rasa nasaba da takun-saka da ake fuskanta akan batun rage tallafin wuta da ruwa a wannan kasa.

A wani lokaci yau Litinin ake sa ran karamin yarima mai jiran gado Mohammed Ben Salmane zai gabatar da shirin gwamnatin kasar daya shafi tattalin arziki, rayiwar jama'a da ci gaban kasa dake da gurin samar da wasu dabaru da hanyoyin inganta tattalin arzikin kasar wanda ba zai dogara kacaukam ba kan man fetir.