Dala Biliyan 8 Ta Fice Daga Nahiyar Afirka A Shekara Guda
Dala Biliyan 8 ce Ta Fice Daga Nahiyar Afirka A Shekara Guda.
An bayyana cewa a kowace shekara nahiyar Afirka tana asarar Dala Biliyan 8 na hannun jarinta.
Kamfanin Dillancin Labarun Xinhua ya ambato tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu, Thabo Mbeki yana cewa; Abin takaici ne cewa a kowace shekara dalar Amurka biliyan 8 ce ta ke ficewa daga nahiyar Afirkan ta hanyar da ta sabawa doka.
Tsohon shugaban kasar Afirka ta kudun ya ci gaba da cea; Wajibi ne a samo hanyoyin da za a dauka domin hana ficewar makudan kudaden na hannun jari daga cikin nahiyar ta Afirka.
Babban Bankin Bada Lamuni Na Duniya ma dai ya fitar da wani rahoto da a ciki ta bayyana asarar makudan kudaden da nahiyar ta Afirka ta ke yi a kowace shekara.