An Kai Harin kunar Bakin Wake A Turkiyya
-
wata \'yar kunar bakin wake mai shekaru 25 ce ta kai harin
Rahotanni daga Turkiyya na cewa wata 'yar kunar bakin wake ta jikkata mutane 17 bayan da ta tarwasa kan ta a wani sansanin yawan bude ido dake birnin Bursa a arewa maso yammacin kasar.
kafofin yada labarai daga kasar sun rawaito cewa lamarin ya auku ne a harabar masalacin Ulu Cami mai muhimanci a yankin.
Da yake tabbatar ministan lafiya na kasar Mehmet Müezzinoglu ya ce babu wata damuwa dangane da yanayin lafiyar mutanen da suka jikkata, wanda mafi yawancin su baraguzan gilasai ne suka yi masu rauni.
ministan ya kara da cewa 'yar kunar bakin waken mai shekaru 25 ta hallaka nan take bayan tarwasa bama-baman da tayi jigida dasu.
Wannan dai na zuwa ne a washe garin sabon gargadin da offishin jakadancin Amurka a Ankara yayi na yiyuwar kai hare-hare.
A wannan shekra dai Kasar Turkiyya ta fuskanci hare-hare boma-bomai da dama musamen a biranen Satambul da Ankara wanda kungiyar 'yan ta'ada ke daukan al'hakin kaiwa.