'Yan Kungiyar PKK Sun Hallaka Wasu Sojojin Kasar Turkiyya 4
(last modified Sun, 01 May 2016 16:51:43 GMT )
May 01, 2016 16:51 UTC
  • 'Yan Kungiyar PKK Sun Hallaka Wasu Sojojin Kasar Turkiyya 4

Rahotanni daga kasar Turkiyya sun bayyana cewar alal kalla sojojin kasar Turkiyya guda hudu sun mutu kana wasu da dama kuma sun sami raunuka sakamakon wasu hare-hare da 'yan kungiyar PKK ta Kurdawa da gwamnatin ta haramta suka kai wa dakarun gwamnatin a yankunan Gaziantep da Mardin da ke kudu maso gabashin kasar ta Turkiyya.

Majiyar tsaron kasar ta Turkiyya ta ce mayakan kungiyar ta PKK sun kai hare-haren ne kan sojojin a lokacin da suka kai wani samame garin Nusaybin da ke kimanin kilomita 792 daga birnin Ankara, babban birnin kasar, inda suka hallaka wasu sojoji uku da kuma raunata wasu 14. Hakan kuwa ya zo ne bayan da 'yan kungiyar suka kashe wani sojan a jiya Asabar.

A bangare guda kuma, 'yan kungiyar ta PKK sun kashe wasu 'yan sandan kasar ta Turkiyya su biyu da kuma raunana wasu kimanin 22 mafiya yawansu 'yan sandan bayan da suka tada da wata mota da suka makare ta da bama-bamai, a kusa da wani ofishin 'yan sanda da ke garin Gaziantep da ke kudancin kasar ta Turkiyya.

A watan Yulin shekarar da ta gabata ce dai yarjejeniyar sulhun da aka cimma tsakanin gwamnatin Turkiyyan da 'yan kungiyar ta PKK ta ruguje, lamarin da ya haifar da ci gaba da kai hare-haren da 'yan kungiyar suke kai wa jami'an tsaron kasar ta Turkiyya. Kasar Turkiyyan dai tana ci gaba da fuskantar hare-hare daga kungiyar ta PKK da kuma Da'esh a wani abin da ake ganin kamar shika ne ta fara komawa kan mashekiya sakamakon goyon bayan ayyukan ta'addanci da gwamnatin Turkiyya take yi a kasashen Iraki da Siriya.