Kisan wani Dan Sandar Saudiya A Birnin Makka
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i4831-kisan_wani_dan_sandar_saudiya_a_birnin_makka
An Kashe Jami'in Dan Sandar Saudiya a Birnin Makka
(last modified 2018-08-22T06:58:14+00:00 )
May 06, 2016 05:57 UTC
  • Kisan wani Dan Sandar Saudiya A Birnin Makka

An Kashe Jami'in Dan Sandar Saudiya a Birnin Makka

Kamfanin dillancin Labaran Was na Saudiya ya nakalto Kakakin Jami'an 'yan sanda na birnin Makka na cewa a daren jiya Alkhamis wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun bindige wani jami'in 'yan sanda a cikin garin na Makka.

Kafin aukuwar wannan lamari, Ma'aikatar cikin gidan Saudiya ta sanar da cewa Jami'an 'yan sandar kasar sun hallaka wasu Mutane 4 dake ake zarkin 'yan ta'adda ne a yayin musayar wuta tsakanin su.

Masarautar Ali-sa'oud da ta kirkiro tare da taimakawa kungiyoyin 'yan ta'adda a Duniya, domin badda tunani mutane ta shiga cikin sahun kasashen dake yaki da 'yan ta'adda kalkashin kasar Amurka a kasashen Siriya da Iraki.