Hadin Gwiwan Saudiyya Da Isra'ila Wajen Cutar Da Al'ummar Palastinu
(last modified Mon, 09 May 2016 04:45:01 GMT )
May 09, 2016 04:45 UTC
  • Hadin Gwiwan Saudiyya Da Isra'ila Wajen Cutar Da Al'ummar Palastinu

A daidai lokacin da wasu kafafen watsa labarai suke ci gaba da fasa kwai dangane da boyayyiyar alaka da aiki tare da ke gudana tsakanin Saudiyya da haramtacciyar kasar Isra'ila, tsohon shugaban hukumar leken asirin haramtacciyar kasar Isra'ilan (MOSSAD), ya tabbatar da ingancin wadannan labarai.

A wani jawabi da ya gabatar a jami'ar Harvard ta Amurka, tsohon shugaban hukumar MOSSAD din Tamir Pardo ya bayyana cewar akwai kyakkyawar alaka da kuma hadin gwiwa da aiki tare tsakanin haramtacciyar kasar Isra'ila da gwamnatin Saudiyya, yana mai bayyana cewar babbar hatsarin da ke fuskantar Isra'ilan shi ne kawai rikicin Palastinawa (a takaice dai yanzu ba ta kasashen larabawa ake yi ba).

Cikin 'yan watannin baya-bayan nan dai kafafen watsa labarai da dama sun yi ishara da wata boyayyiya kuma dadaddiyar alaka da aiki tare da ke gudana tsakanin gwamnatin Saudiyya da haramtacciyar kasar Isra'ila, babbar manufar hakan kuwa ita ce fada da Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma kawo karshen kungiyoyin gwagwarmaya masu adawa da bakar siyasar mamaya ta yahudawan sahyoniya; kamar yadda tsohon shugaban hukumar leken asirin Saudiyyan Turki Faisal da tsohon mai ba wa firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ilan shawara kan harkokin tsaron Manjo Janar Yaakov Amidror (rtd) suka tabbatar da hakan cikin mukabalar da suka yi a tsakaninsu a cibiyar "Washington Institute For Near East Policy" da ke birnin Washington na Amurka.

Har ila yau a baya-bayan nan kafar watsa labaran Bloomberg ta Amurka ta rubuta cewa cikin shekaru biyun da suka gabata wato tun daga 2014, wakilan gwamnatin Saudiyya da ta Isra'ila sun gudanar da wasu tarurruka na sirri masu muhimmanci har sau biyar a kasashen Indiya, Italiya da Jamhuriyar Chezch, babban abin da suka tattaunawa kuwa shi ne batun Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayin abokiyar gaban da suka yi tarayya kanta.

Masana dai suna ganin cewa cikin shekarun baya-bayan nan kasar Saudiyya, a matsayinta na kasar musulmi kana kuma wacce take dauke da wajaje biyu mafiya tsarki a Musulunci wato Dakin Ka'aba da Masallacin Annabi (s) ta aiwatar da wasu siyasosi wadanda suka zamanto babbar cutarwa ga duniyar musulmi da kuma su kansu al'ummar musulmin na duniya. Daya daga cikinsu kuwa shi ne irin wannan hadin gwuiwa da aiki tare da take yi da haramtacciyar kasar Isra'ila a matsayinta na babbar makiyar al'ummar musulmi.

A matsayin misali kungiyar hadin kan kasashen musulmi (OIC), wacce aka kirkiro ta da nufin goyon bayan lamurran Palastinawa da kare hakkokinsu, amma a halin yanzu gwamnatin Saudiyya ta mayar da kungiyar ta zamanto wata cibiya ta kulla makirci ga kasashen musulmi da rufe ido kan matsalar Palastinawan. Baya ga amfani da kudi wajen sayen jagororin kasashen larabawa a tarurrukan kungiyar hadin kan kasashen larabawa da ta kungiyar hadin gwiwan kasashen larabawan Tekun Fasha, duk dai da nufin tabbatar da siyasarsu ta goyon bayan manufofin haramtacciyar kasar Isra'ila; daya daga cikin irin wadannan manufofin kuwa shi ne bayyana kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon a matsayin kungiyar ta'addanci da wadannan kungiyoyi biyun suka yi a biya matsin lambar Saudiyya.

Ko shakka babu, kamar yadda shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon din Sayyid Hasan Nasrallah ya fadi ne ewa, a halin yanzu dai kasar Saudiyya ta zamanto ja-gaban shirin fada da kungiyoyin gwagwarmaya masu adawa da haramtacciyar kasar Isra'ila a yankin Gabas ta tsakiya. Wanda babu wanda wannan siyasar ta Saudiyya za ta amfanar in ban da haramtacciyar kasar Isra'ila.