Harin Ta'addancin Kungiyar Da'ish A Birnin Riyad Na Kasar Saudiyya
Kungiyar ta’addanci ta Da’ish ta dauki alhakin kai harin bom a birnin Riyad fadar mulkin kasar Saudiyya a jiya Litinin.
Majiyar rundunar ‘yan sandan Saudiyya a jiya Litinin ta sanar da cewa; Motar wani mutum ta tarwatsewa a kofar gidansa da ke yankin Aziziyya amma dai babu hasarar rai da tarwatsewar motar ta janyo, sai dai konewar wasu motoci da suke wajen da bom din ya tashi.
A bayan faruwar tarwatsewar bom din kungiyar ta’addanci ta Da’ish ta fitar da bayanin cewa; Ita ce ke da alhakin dana bom din a jikin motar a kokarin da kungiyar key i na halaka mai motar saboda kasancewarsa jami’in tsaron kasar ta Saudiyya.
A ranar 29 ga watan Janairun da ya gabata ma kungiyar ta’addanci ta Da’ish ta kai wani mummunan harin wuce gona da iri kan Masallacin ‘yan shi’a a yankin Sharkiyya na kasar ta Saudiyya, inda harin yay i sanadiyyar mutuwar mutane 4 tare da jikkata wasu 18 na daban.