Labanon : Hizbullah Ta Sanar Da Shahadar Babban Kwamandan Sojinta
(last modified Fri, 13 May 2016 05:31:18 GMT )
May 13, 2016 05:31 UTC
  • Shahid Mustafa Badruddeen na Hizbullah
    Shahid Mustafa Badruddeen na Hizbullah

Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta sanar da cewa babban kwamandan bangaren sojinta Shahid Mustafa Badruddeen yayi shahada sakamakon wani harin da haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai wa daya daga cikin cibiyoyinta da ke kusa da filin jirgin saman birnin Damaskus na kasar Siriya.

Kungiyar ta Hizbullah ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar da safiyar yau Juma'a inda ta ce cikin dukkanin alhari take sanar da shahadar babban mujahidi Shahid Mustafa Badrudden (wanda aka fi sani da Sayyid Zulfiqar) sakamakon wani hari da aka kai wa cibiyar kungiyar da ke kusa da filin jirgin saman Damaskus, na kasar Siriya.

Sanarwar ta kara da cewa shi dai Shahid Badrudden yana kasar Siriyan don jagorantar fadar da kungiyar take yi da kungiyoyin 'yan ta'adda masu kafirta musulmi da aka shigo da su kasar Siriyan don cimma manufofin Amurka da yahudawan sahyoniya a yankin Gabas ta tsakiya.

Har ila yau sanarwar ta ce tuni ta fara gudanar da bincike don tantance yanayin harin, tana mai cewa a nan gaba za ta yi karin haske kan lamarin.

Shi dai Shahid Badrudden ya zama kwamandan sojin kungiyar ta Hizbullah ne bayan shahadar tsohon kwamandan sojin Shahid Emad Mughniyya wanda haramtacciyar kasar Isra'ilan ta kashe a kasar Siriya a shekara ta 2008.