Rasha Ta Jaddada Muhimmancin Yanke Taimako Ga 'Yan ta'adda.
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta bayyana muhimmancin yanke hanyoyin taimakawa kungiyoyin ta'adda.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova, ta fada a yau asabar cewa; dole ne a yanke hanyoyin da 'yan ta'addar kasar syria su ke samun taimako daga waje, tare da jaddada cewa; hanyar Turkiya ce ginshikin wurin da 'yan ta'addar su ke samun taimako.
Zakharova ta ci gaba da cewa; Warware matsalar kasar Syrai yana da alaka ne da yadda kasashen da su ke da tasiri akan kungiyoyin da su ke cikin kasar ta syria.
A gefe daya, cibiyar ta ke kula da sulhunta masu fada da juna a kasar ta Syria, ta ce fiye da 'yan ta'addar kungiyar Jubhatun-Nusrah 100 ne s ka shiga Syria daga iyakar Turkiya.