Tattaunawa Tsakanin Ministan Harkokin Wajen Rasha Da Takwaransa Na Masar
May 22, 2016 05:54 UTC
Kasashen Rasha da Masar Sun tattauna akan Syria da Palasdinu
A yau lahadi an yi tattaunawa a tsakanin ministocin harkokin Wajen kasashen Rasha da Masar ta wayar tarho dangane da halin da kasar Syria ta ke ciki, haka nan kuma yankin palasdinu.
Sargey Lavrov na Rasha ya shaidawa takwaransa na Masar Samih Shukry cewa kasarsa za ta ci gaba da goyon bayan Syria domin samun mafitar siyasar a karkashin dokokin kasa da kasa.
Lavrov ya kuma yi musayar ra'ayi da Samih Shukry na masar din akan taron kasa da kasa da aka yi akan kasar Libya a ranar 16 ga watan Mayu.
Akan Palasdinu ma bangarorin biyu sun jaddada muhammancin samun mafita.
Tags