Turkiyya : Bam Ya Kashe 'Yan Kashe Sojoji Shida
Rindinar sojin kasar Turkiyya ta sanar ta mutuwar wasu sojoji shida da wasu biyu na daban suka raunana a harin wani bam da aka kai kan tawagar motocinsu a kudu maso gabashin kasar.
Tuni dai aka ce kungiyar kurdawan nan ta PKK ce keda alhakin kai wannan harin.
Wani babban jami'in soji ya tabbatarwa da kanfanin dilancin labaren AFP cewa bayan harin bom din an kuma yi ta harbo rokoki kan ayarin motocin soji a yankin na Van.
Rindinar sojin Turkiyya ta ce ta kai farmaki da jiragen sama bayan harin.
Yankin kudu maso gabashin Turkiyya dai ya jima yana fama da rikice rikice tsakanin jami'an tsaro Turkiyya da 'yan tawayen Kurdawa na PKK.
A cikin shirin sa daya gabatarwa al'umma, sabon firayi ministan kasar Binali Yildirim, ya sha alwashin yaki da duk wasu masu tada kayar baya a duk fadin kasar.