Halakar 'Yan'taadda Fiye da 40 A Kasar Masar.
Feb 11, 2016 05:33 UTC
Fiye Da 'yan ta'adda 40 ne su ka halaka a yankin Sina na kasar Masar.
Kamfanin Dillancin Labarun Spotik na kasar Rasha ya ambato cewa; A jiya laraba jiragen sama masu saukar angulu sun yi aman wuta a wata mabuya ta 'yan ta'addar kungiyar Da'esh a yankin Sina.
Sojan Masar Sun sanar da cewa; Sun kai harin ne bayan wani hari da aka kai wa motarsu ta soja a kudancin garin Sheik Zuwaid. Harin na sojan Masar ya yi wa 'yan ta'addar asara mai yawa.
Tun a cikin watan Decemba na 2013 ne sojojin Masar su ka bude kai hare-hare masu tsanani akan kungiyoyin da su ke dauke da makamai a yankin Sina ta arewa.
Tags