Turkiyya : An Sake Kaiwa 'Yan Sanda Hari
Jun 08, 2016 10:51 UTC
Rahotanni daga Turkiyya na cewa mutane uku ne suka rasa raykansu sakamakon wani harin bom da aka kai da mota a kudu maso gabashin kasar.
An dai kai harin ne a wania barikin 'yan sanda dake yankin Midyat, inda dan sanda guda da fararen hula biyu suka mutu, kamar yadda firimiya ministan kasar Binali Yildirim ya sanar.
Kawo yanzu babu wata kungiya data dau alhakin kai harin, sai dai tuni gwamnatin kasar ta dora alhakinsa ga kungiyar Kurdawan nan ta PKK.
Wannan harin dai na zuwa kwana guda bayan wani makamancinsa da yayi sanadin mutuwar mutane akalla 11 ciki harda 'yan sanda a birnin Santambul.
Tags