Ziyarar Shugaban Kasar Ghana A Anan Iran.
Shugaban Kasar Ghana John Dramani Mahama ya kawo ziyarar aiki nan Iran.
Ziyarar shugaban kasar ta ta Ghana John Dramani Mahama ta zo ne bisa gayyatar da takwaransa na Iran Dr. Hassan Rauhani ya yi masa, domin bunkasa alakar kasashen biyu.
Shugaba Mahama wanda ya ke tare da tawaga ta 'yan siyasa da tattalin arziki, ya sami tarbar ministan gona kuma shugaban kwamitin hadin guiwa a tsakanin Iran da Ghana, Muhammad Hujjaty, a filin saukar jiragen sama na Mehrabad.
A gobe lahadi ne dai shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani zai karbi bakuncin takwaran nashi na Gahan a gwamnatance.
Daga cikin wadanda shugaban na Ghana zai gana da su da akwai jagoran juyin juya halin musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamnei.