Turkiya Ta Nemi Gafarar Kasar Rasha
Urdugan Ya Nemi Gafarar Putin Akan Harbo Jirgin Saman Rasha.
Kamfanin Dillancin Labarun Faransa ya ambato majiyar fadar gwamnatin Rasha na cewa; Shugaban Turkiya Rajab Tayyab Urdugan, ya nemi gafarar takwaransa na Rasha Vladimir Putin akan harbon jigin yakin Turkiyan a cikin 2015.
A ranar 24 ga watan Nuwamba na 2015 ne dai jiragen yakin Turkiya su ka kakkabo jirgin Rasha samfurin Sukhoi 24 a kan iyakar Turkiyan da Syria, wanda ya yi sanadin mutuwar matukin jirgin.
Alaka a tsakanin Ankara da Moscow ta yi kamari sanadiyyar lamabrin.
Sai dai a yau litinin Fadar Kremline ta ce; Urdugan ya nuna juyayinsa da ta'aziyyarsa ga iyalan matukin jirgin yakin na Rasha, sannan kuma ya nemi gafara."
Kakakin fadar Krimline Dmitry Viscov ya ce; Urdugan ya kuma ce zai duk kokarin da zai iya yi, domin ganin alaka tsakanin kasashen biyu ta gyaru.