Erdogan Zai Gana Da Putin A Wannan Mako
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i7351-erdogan_zai_gana_da_putin_a_wannan_mako
Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, zai gana da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a wannan mako.
(last modified 2018-08-22T11:28:30+00:00 )
Jun 28, 2016 06:23 UTC
  • Erdogan Zai Gana Da Putin A Wannan Mako

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, zai gana da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a wannan mako.

Firaministan kasar Turkiya ne Binali Yildirim ya sanar da hakan yana mai cewa ranar Laraba ko Alhamis Erdogan zai gana da Putin, sai dai ba tare da yin wani karin haske ba, kamar yadda Jaridar kasar ta Turkiyya ''Dailysaba'' ta rawaito.

Mr Erdogan na fatan maido da kyaukyawar alaka tsakanin kasashen biyu cikin gajeren lokaci bayan nadamarsa akan kakkabo jirgin sojin Rasha da Turkiyya tayi a bara.

A ranar 24 ga watan Nuwamba na 2015 ne dai jiragen yakin Turkiya su ka kakkabo jirgin na Rasha samfurin Sukhoi-Su- 24 a kan iyakar Turkiyan da Syria, wanda ya yi sanadin mutuwar matukin jirgin.

A lokacin dai Turkiyya ta zargi jiragen yaki rasha da keta sararin samaniyyar ta ba kakkautawa, lamarin daya sa ta dau matakin kakkabo jirgin.