Kungiyar Hizbullah Ta Yi Allawadai Da Hare-Haren Istanbul
Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta fitar da wani bayani a yau, wanda a cikinsa ta yi Allawadai da hare-haren da aka kai kan babban filin safka da tashin jiragen sama na birnin Istanbul na kasar Turkiya.
A cikin bayanin da kungiyar ta Hizbullah ta fitar ta bayyana cewa, wadannan hare-hare abin Allawadai ne, kuma hakan ya zama babban dalili da ke tabbatar da cewa 'yan ta'adda masu dauke da mummunar akidar takfiriyya ta'addancinsu zai iya shafar kowane irin mutum ba tare da banbanci ba, domin kuwa ta'addanci ba shi da addini, kuma yana kiyayya ne da mutum a matsayinsa na dan adam, wanda hakan ke kara tabbatar da wajabcin hada karfi tsakanin al'ummomin musamman na musulmi domin fuskantar wannan babbar annoba.
Bayanin ya kara da cewa wadanda suke amfani da batun ta'addanci domin cimma manufofi na siyasa ko kuma bangaranci na akida da banbancin mazahaba, lokaci da ya kamata su ajiye wannan a gefe domin fuskantar hatsarin da su ma ba zai bar su ba komai jimawa.
Harin da aka kaddamar a kan babban filin safka da tashin jiragen sama na Kamal Ataturk da ke birnin Istanbul a tsakar daren jiya, ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 41, yayin da wasu da dama kuma suka samu raunuka, babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, amma mahukuntan kasar Turkiya dai sun nuna yatsan tuhuma akan kungiyar ISIS